Hausa poems followed by their translations:
YAWON DUNIYA
Jiya a yawon duniya
Na hadu da karamin mutum
Zan rera waka ga mai so na
Mai ajiyar karamin mutum
Dan lele zo mu yi lilo mu gangaro
Alawa ga zaki ga gardi
Sai karamin mutum
Yaushe za ka ziyarci fadata
Don nayi maka shimfidar lagwada
Ya mai so na
Sadaukar min da karamin mutum
Don na ga fararen taurari
THE VOYAGE
In my voyage in yesteryears
I met the small statured one
One who loved me and for whom I sing a song
The keeper of the small one
The affectionate one come go with me
Oh you the sweet and the delicious
Oh you the small one
When shall you come see my palace?
When do you come for a grand treat?
Oh you my lover
Give me yourself the small one
Come give me ecstasy
===========================
HARUFFAI SHIDA
Haruffai shida masu fararen furanni
Na yi kitso da tsagun ko wane daya
Harafi na daya: inibin raina
Sukari a shafin kirjina
Mangwaro koshi babu
Abarba gidan zaki
Idon basirana
Lafazin rayuwata
Malam bude littafi
tarbo min haruffan nan shida
Kafin na rikice
THE SIX LETTERS
Six letters with white flowers
Each being a part of me
One is the vineyard of my soul
The second the sugar of my heart
The third an insatiable fruit
The fourth is oozing juice
The fifth is my intellect
The sixth the basis of my existence
Open your book and
Lead me to the six letters
Lest I vanish.
===========================
BARIN ZUMA
Sannu sannu zan bi gabobinka dai bayan dai
Amma sai nai maka barin zuma
Sannan harshe na ya bika da lasa
Tun daga sama har kasa
Ba inda zan bari face sai na cimma burina
Sai ka narke gumin jikinka
Ya kashe min kishi.
A SWEET LICK
Slowly I’ll go down your limbs
After I’ve covered you in honey
My tongue shall roll over you
Up and down
Leaving out no portion of you
Till I devour your sweat
And quench my thirst.
===========================
YANCI
Nonuwana sun cika sun yi nauyi
Suna begen hannayenka
Kai kadai ka iya rikesu
Tamkar kana rike da kwai
Kai ka iya murza su kamar amaro
Ka iya shan su kamar lemu
Yaya zanyi da raina?
Ai ba sauran budurci a tare da nonuwa na
Tun ranar da ka ba su ‘yanci
Basu san kowa ba sai kai.
FREEDOM
Full and heavy my breasts
Yearn for your touch
You know best how to handle them
In a delicate way
In a firm squeeze
And juicy suckle
Oh my my
No more uninitiated they are
For you’ve set them free
Knowing no one but you.
===========================
GWAGWARMAYAR KAUNA
Na bude idona
Haske kamar na walkiya ya keto
Don ganinka.
Lebe na karkarwar murna
Baki zai sha zumar bakin masoyi
Kai!
Irin wannan lagwada
Ga zuma
Ga kuma madara za ta kwarara
Jiki fa ya rude
Samun natsuwa fa sai masoyi da masoyiya
Sun dulmiya a cikin gwagwarmayar kauna
Sai sun hade. . .
THE LOVE BATTLE
My eyes wide open
Full of glimmer
Just to behold you
The tremor in my lips
Grows, anticipating a kiss
From a lover, oh!
What a delicacy
How sweet
Such flowing cream
The trembling soul
Knows no peace till lovers meet
And delve in the battle of love
Together…
===========================
Poems & Translations (c) Ismail Bala
TIRKASHI!!!!! Na gaba yayi gaba.
ko hakane
Allah ya Kara lafiya da nisan kwana Mai amfani.
love.
Freedom tayi lol!
Ismail, this is really good. some of the lines read as beautiful as Rumi’s love poems. Nice to know you are taking an interest in this.
ALLAH TA TAIMAKA
kai freedom tahadu sosai
ABUN YAYE KYAU KENAN
Me zaki iya cewa akan shi wannan freedom.
CUTE
This is really good and I don’t understand a word of hausa !
HARUFFAI SHIDA is especially beautiful.
THANK YOU SO MUCH!
Wani Abu sai soyyaya
Nice one .Allah ya sarki
yayi daidai…
Nice.1
Hmmm!